Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana sunayen ‘yan takarar kujerar Sanata guda 47 da ba su samu amincewar shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar ba gabanin babban zaben 2027.
An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an gudanar da tantancewar ne bisa tsare-tsare da ka’idojin jam’iyyar.
Daga cikin fitattun wadanda ba su tsallake ba akwai tsohon Sanata mai wakiltar Bayelsa East, Ben Murray-Bruce, da kuma Benson Agadaga.
Jihar Rivers West ce ta fi yawan wadanda aka hana takara, inda mutane hudu suka fada cikin jerin, ciki har da Oyukaye Flag Amachree, Tamunobaabo Wemike Danagogo, Jack-Rich Tein, da Banigo Ipalibo.
Haka kuma, Jihar Zamfara ta samu mutane bakwai daga mazabun Central, North, da West da ba su samu sahalewa ba.
Sai dai APC ba ta bayyana dalilan da suka sa aka hana wadannan ‘yan takara shiga zaben fidda gwani ba.
