Hukumar Kula da Wasanni ta Kasa (NSC) ta taya tawagar ‘yan wasan daga nauyi ta Najeriya murna bayan gagarumar nasarar da suka samu a Gasar African Senior Weightlifting Championship ta 2026 da aka gudanar a Ismailia, kasar Masar.
Najeriya ta kammala gasar da jimillar lambobin yabo 29, wadanda suka hada da zinare 14, azurfa 13, da tagulla biyu, lamarin da ya kara nuna irin ci gaban da kasar ke samu a harkar wasanni.
Shugaban NSC, Mallam Shehu Dikko, ya bayyana cewa wannan bajinta wata babbar shaida ce da ke nuna cewa harkar wasannin Najeriya na tafiya a kan turba mai kyau.
Ya yabawa ‘yan wasan bisa jarumtaka, kwarewa, da kishin kasa da suka nuna a yayin gasar, yana mai cewa wannan nasara ba wai ta wasan daga nauyi kadai ba ce, har ma da daukacin Najeriya baki daya.
Daraktan Janar na NSC, Bukola Olopade, shi ma ya jaddada cewa kokarin tawagar ya nuna yadda Najeriya ke kara zama karfen kafa a wasannin Afirka.
A bangaren mata, Najeriya ta samu matsayi na uku, inda fitattun ‘yan wasa kamar Ruth Asuquo Nyong, Onome Omolola Didih, da Rafiatu Folashade Lawal suka taka muhimmiyar rawa wajen lashe lambobin zinare da dama.
A bangaren maza kuwa, Favour Omovigho Agboro, Edidiong Joseph Umoafia, da Lucky Joseph sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara yawan lambobin yabo.
Hukumar ta yabawa masu horaswa da jami’an tawagar, tana mai bayyana cewa wannan nasara za ta zama abin karfafa gwiwa ga sauran ‘yan wasan Najeriya domin ci gaba da daga martabar kasa a manyan wasanni na duniya.
