Adebayo Adeyemi Rashidat ta zama zakara a gasar Ogun Women Run 2026, gasar tseren kilomita 5 (5km) da aka ware domin mata, wadda kamfanin Brussel Sports Management Limited ya shirya.
Ta kammala tseren ne da lokaci mai kyau na 30:15.61 a ranar Asabar, inda ta doke sauran ‘yan takara da dama.
Gasar mai kayatarwa wadda aka gudanar a birnin Abeokuta, ta samu halartar kusan mata 1,000. An fara tseren ne daga Sapon, inda aka kammala a MKO Abiola Sports Arena, tare da manufar inganta lafiyar jiki, walwala da kuma karfafa gwiwar mata.
A matsayi na biyu, Alawode Omotayo Adiat ta zo da lokaci na 31:09.46, yayin da Akoni Oluwanifemi ta zo ta uku da 31:18.65.
Saboda wannan nasara, Rashidat ta samu kyautar kuɗi har ₦500,000, yayin da wadda ta zo ta biyu ta samu ₦300,000, sannan ta uku ta karɓi ₦200,000.
Bayan kammala gasar, Manajan Darakta na Brussel Sports Management Limited, Mrs Yetunde Johnson, ta bayyana farin cikinta kan yadda taron ya gudana cikin nasara.
Ta ce:
“Mun yi matuƙar farin ciki da yadda gasar ta gudana yau. Halartar mutane ya burge mu sosai, kuma komai ya tafi cikin tsari. Ina gode wa ƙungiyata, Gwamnatin Jihar Ogun da kuma dukkan masu daukar nauyin wannan shiri.”
