Gwamnatin Jihar Kogi ta mayar da martani kan wata muryar sauti da ta yadu a kafafen sada zumunta, wadda ake dangantawa da wata ma’aikaciyar gwamnati, inda ta nuna damuwa kan zargin cewa ana ware matasan Ebira daga samun guraben aiki a cikin ma’aikatar gwamnatin jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Ahmed Ododo ta ginu ne a kan manufofin hada kai, sauraron jama’a, tattaunawa mai amfani da kuma shugabanci mai daukar mataki.
Fanwo ya ce gwamnati ta lura da yadda jama’a ke mayar da martani kan wannan murya da kuma wani bidiyo da ke yawo dangane da lamarin.
Ya kara da cewa Gwamna Ododo shugaba ne mai yi wa jama’a hidima, wanda aka zabe shi ta hanyar kuri’a, kuma yana da kudurin tabbatar da adalci da daidaito ga kowa.
A cewarsa, duk da cewa abin da aka fada a cikin muryar ra’ayin mutum ne, wanda doka ta ba da damar fadar sa, amma akwai hanyoyin da aka tanada da ya kamata ma’aikatan gwamnati su bi wajen gabatar da koke-kokensu.
“Duk da haka, wannan gwamnati na mutunta ‘yancin fadar albarkacin baki, kuma ba za ta take ko hukunta kowane dan kasa ba saboda ya bayyana ra’ayinsa cikin lumana,” in ji sanarwar.
Sai dai ya nuna damuwa cewa wasu mutane da kungiyoyi na kokarin mayar da lamarin abin tada hankali ta hanyar yada shi fiye da kima.
Gwamnatin ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da adalci, hadin kai da kuma bai wa kowa dama iri daya a fadin jihar.
