Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Osun ta gudanar da babban taronta na jiha a ranar Asabar, inda aka zabi sabbin shugabanni.
Taron ya gudana ne a birnin Osogbo, babban birnin jihar, tare da halartar wakilai daga kananan hukumomi 30 na jihar. An tsaurara matakan tsaro sosai yayin taron, inda ‘yan sanda da jami’an DSS suka kasance a wurin.
Shugaban kwamitin taron ADC, Mudashiru Akinlabi, ne ya jagoranci aikin zaben.
A yayin taron, an zabi shugabanni da dama ta hanyar amincewa (consensus), ciki har da:
Issa Adesiji – Shugaban jam’iyya
Lani Baderinwa – Sakatare
Adepeju Adigun – Ma’aji
Funmilade Oyebode – Shugabar Mata
Ademola Owoade – Shugaban Matasa
Oluwaseun Abosede – Mai magana da yawun jam’iyya
A jawabinsa na karɓar matsayi, sabon shugaban ADC na jihar Osun, Issa Adesiji, ya bukaci mambobin jam’iyyar su shirya tsaf domin zaben gwamna da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.
Ya ce dole ADC ta yi aiki tukuru domin lashe zaben, tare da kira ga hadin kai da goyon baya ga dan takarar gwamna na jam’iyyar, Najeem Salaam.
