Kungiyar kare hakkin jama’a da yaki da rashawa ta SERAP ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya umarci a binciki zargin bacewar kudade har ₦2.9 biliyan daga hukumomin NIGCOMSAT da NNRA.
Kungiyar ta kuma bukaci Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dakta Bosun Tijani, da ya bayyana inda kudaden suke. Haka kuma ta roki Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, tare da hukumomin yaki da rashawa, da su fara bincike cikin gaggawa.
A cewar SERAP, an bayyana wadannan zarge-zarge ne a cikin rahoton Auditor-General na shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa kamfanin NIGCOMSAT ya kasa bayyana yadda aka kashe sama da ₦465 miliyan da aka zuba jari a kamfanin Gicell Wireless Ltd ba tare da cikakken izini ko takardu ba. Wannan ya jawo zargin cewa kudin na iya kasancewa an karkatar da shi.
Har ila yau, an zargi hukumar da yin wasu kudade marasa ka’ida ga ma’aikata, da kuma kasa mayar da sama da ₦507 miliyan na kudaden shiga ga gwamnati. Sauran matsaloli sun hada da bashi sama da ₦1.6 biliyan da ba a karbo ba, da kuma wasu kudade da ba a san inda suka shiga ba.
A bangaren NNRA kuma, an ce hukumar ta kashe miliyoyin kudade kan horaswa ba tare da wata hujja da ke nuna cewa an gudanar da horaswar ba. Haka kuma an yi wasu biyan kudi kan kayan ICT ba tare da izini ba.
SERAP ta jaddada cewa dole ne jami’an gwamnati su kasance masu gaskiya da rikon amana wajen kula da kudin jama’a. Ta kuma yi gargadin cewa za ta dauki matakin shari’a idan ba a dauki mataki cikin kwanaki bakwai ba.
