Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a taron ADVANCE Workers, Pastors and Leaders Conference da aka gudanar a Transforming Church International, Abuja.
A cikin jawabin nasa mai taken “Rawar da coci ke takawa wajen sauya al’umma”, Otti ya ce yawan mutanen da ke kaucewa siyasa saboda suna kallonta a matsayin “datti” na daya daga cikin dalilan da suka jawo matsalolin shugabanci a Najeriya.
Ya jaddada cewa:
“Siyasa wata muhimmiyar hanya ce da ake amfani da ita wajen zabar shugabanni da kuma tsara makomar al’umma.”
Ya kara da cewa duk wanda ke son ganin ingantacciyar gwamnati dole ne ya shiga cikin harkokin siyasa maimakon zama mai kallo kawai.
