Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da shirin gudanar da aikin jinya kyauta (medical outreach) tare da hadin gwiwar kungiyar likitocin Najeriya da ke zaune a Amurka (Association of Nigerian Physicians in the Americas – ANPA), wanda zai fara daga ranar 13 ga watan Afrilu.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Enoch Uche, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a birnin Umuahia yayin wani taron manema labarai gabanin fara shirin, wanda zai gudana har zuwa ranar 17 ga watan Afrilu, 2026.
Ya bayyana cewa kimanin likitoci 25 daga Amurka za su halarci shirin, inda za su gudanar da tiyata da bada shawarwari kan lafiya kyauta tare da hadin gwiwar likitocin cikin gida.
Uche ya ce an shirya wannan aikin ne bisa umarnin Gwamna Alex Otti, bayan nasarar irin wannan shiri da aka gudanar shekaru biyu da suka gabata.
A cewarsa, wannan shiri na daga cikin manufofin gwamnatin jihar na hada kai da likitocin Najeriya da ke kasashen waje domin inganta samun ingantacciyar kiwon lafiya mai saukin kudi ga al’umma.
Ya kara da cewa tawagar likitocin za ta isa jihar a ranar 13 ga Afrilu, yayin da za a gudanar da bikin bude shirin a dakin taro na Michael Okpara Auditorium da misalin karfe 12 na rana a ranar 14 ga Afrilu, inda kuma za a fara gudanar da cikakken aikin jinya a ranar.
An ware wurare biyu domin gudanar da shirin, wato:
Asibitin Aba General Hospital
Abia State Specialist Hospital and Diagnostic Centre da ke Umuahia
A cewarsa, za a gudanar da ayyukan da suka shafi ido da tiyatar ido a asibitin Specialist Hospital, yayin da sauran tiyata na gaba daya za su gudana a Aba General Hospital.
