Sabon kocin tawagar ‘yan mata ‘yan kasa da shekara 17 ta Najeriya (Flamingos), Akeem Ishola Busari, ya gayyaci jimillar ‘yan wasa 36 zuwa sansanin horo domin shirye-shiryen fafatawar zagaye na biyu na neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta Mata U-17.
Najeriya za ta kara ne da mai nasara tsakanin Niger Republic da Guinea, inda Niger za ta karbi bakuncin wasan farko na zagaye na daya a wannan karshen mako, yayin da za a buga wasa na biyu a Conakry a mako mai zuwa.
Wanda ya yi nasara a haduwar zai fafata da Najeriya a zagaye na biyu, inda za a buga wasan farko tsakanin ranakun 22 zuwa 24 ga watan Mayu. Flamingos za su karbi bakuncin wasan dawowa a ranar 30 ga watan Mayu.
A cikin jerin ‘yan wasan da aka gayyata, akwai masu tsaron gida biyar, ‘yan baya goma, ‘yan tsakiya 13 da kuma ‘yan gaba takwas.
Busari, wanda ya maye gurbin tsohon koci Bankole Olowookere, na fara sabon tafiyarsa ne tare da tawagar Flamingos, inda ake sa ran zai gina sabuwar kungiya mai karfi.
A halin yanzu, Najeriya na daga cikin kasashen da suka yi fice a baya, bayan samun lambar tagulla a Gasar Kofin Duniya ta Mata U-17 ta shekarar 2022.
Za a gudanar da gasar bana ta FIFA U-17 Women’s World Cup a kasar Morocco daga ranar 17 ga watan Oktoba zuwa 7 ga watan Nuwamba.
