Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi watsi da cece-kuce da suka biyo bayan kalamansa kan ɗan jarida Seun Okinbaloye, inda wasu suka fassara maganarsa a matsayin barazana.
Wike ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da News Central a ranar Litinin, inda ya ce duk wanda ya san irin dangantakarsa da Okinbaloye ba zai ɗauki maganarsa da muhimmanci ba.
Ya ce mutane a Najeriya suna yawan ɗaukar abubuwa fiye da yadda aka faɗa, musamman idan aka shigar da siyasa a ciki.
“Abin takaici ne yadda ake ɗaukar komai a Najeriya da tsanani, musamman idan siyasa ta shiga ciki,” in ji shi.
Ministan ya jaddada cewa kalamansa na cewa zai “harbe shi” ba wata barazana ba ce, illa kawai salon magana ne da ke nuna irin fushin da ya ji a lokacin.
Haka kuma, ya soki Okinbaloye kan yadda bai tuntube shi kai tsaye ba kafin batun ya zama babban abin cece-kuce a bainar jama’a.
A ƙarshe, Wike ya tabbatar da cewa sun riga sun tattauna da juna, kuma babu wata matsala tsakanin su.
Wike ya ce cece-kucen da aka yi kan batun na da alaƙa da siyasa, ba wai ainihin abin da ya faɗa ba.
