Tsohon jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi Okasanmi, ya bukaci a rungumi tsarin intelligence-led policing domin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar.
Ya bayyana cewa duk da wasu matakai da aka ɗauka a baya, har yanzu ba su isa ba wajen kawar da matsalar tsaro gaba ɗaya.
Okasanmi ya ce wannan sabon tsarin ya ta’allaka ne da tattara sahihan bayanai daga jama’a da kuma haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma.
“Intelligence-led policing hanya ce da ke dogara da tattara bayanai. Idan aka samu bayanai daga jama’a, ‘yan sanda za su sarrafa su tare da haɗa kai da shugabannin al’umma domin yaƙar ta’addanci,” in ji shi.
Ya kuma danganta matsalolin da ke hana ‘yan sanda aiki yadda ya kamata a Najeriya da rashin kulawar gwamnati, ƙarancin walwala, da rashin kayan aiki na zamani.
Ya kara da cewa duk lokacin da jami’an ‘yan sandan Najeriya suka je ƙasashen waje domin ayyukan wanzar da zaman lafiya, sukan yi fice tare da samun yabo mai yawa.
“To me ya sa ba za su iya yin irin wannan aiki a gida ba?” ya tambaya.
Okasanmi ya bukaci gwamnati da ta ƙara zuba jari a fannin tsaro, ta hanyar samar da kayan aiki, horo, da kuma inganta rayuwar jami’an tsaro.
Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su daina ɓoye masu laifi, yana mai cewa yawancin masu aikata laifi suna rayuwa ne a cikin al’umma kuma ana san su.
“Wadannan ‘yan bindiga ba fatalwowi ba ne. Mutane ne kamar mu, kuma ana san su. Amma ana ɓoye su saboda alaka ko addini. Wannan dole ne ya tsaya,” in ji shi
