Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro a gidan gwamnati da ke Katsina, sakamakon sabon tashin hankalin da ya kara tayar da hankali a fadin jihar.
Taron wanda ya hada manyan jami’an tsaro ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro daban-daban, shugabannin kananan hukumomi daga yankunan da abin ya shafa, da kuma manyan wakilai daga rundunar sojin Najeriya da hedikwatar tsaro.
Haka kuma, wakilai daga Department of State Services sun halarci taron domin tattauna hanyoyin gaggawa da za a dauka wajen dakile karuwar matsalar tsaro.
Majiyoyi sun bayyana cewa an mayar da hankali ne kan yadda za a kara tsaurara matakan tsaro, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da sabbin hare-hare suka sake tayar da hankulan jama’a, inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan jihar.
Ana sa ran cewa bayan wannan taro, gwamnati za ta fito da sabbin tsare-tsare da matakan da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
