Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Apo, Abuja, ta ba da umarnin ƙwace kadarorin da ake alaƙanta da ‘yar kasuwa Aisha Achimugu tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.
Mai shari’a Jude Onwugbuzie ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis bayan amincewa da buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na a kwace kadarorin na dindindin.
Kadarorin da kotun ta ba da umarnin a ƙwace sun haɗa da:
Kayan ado (jewellery) da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 4.65.
Motoci alfarma guda 11 da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 4.29.
Kuɗi dala 50,000 na Amurka.
Da kuma Naira miliyan 30 a tsabar kuɗi.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Hukumar EFCC ta shigar tana neman a ƙwace waɗannan kadarori domin su koma mallakin Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta amince da buƙatar EFCC, inda ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin gaba ɗaya bisa hukuncin ƙarshe.
