Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, da takwaransa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, sun yi alhinin rasuwar wanda ya kafa All Christians Fellowship Mission, Rev. Dr. William Okoye.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Peter Obi ya bayyana marigayin a matsayin babban jagoran addini wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautar Allah, koyar da gaskiya da kuma gina al’umma.
Obi ya ce Rev. Okoye ya kasance mutum mai tasiri wanda ya zaburar da mutane da dama su rayu cikin gaskiya, ɗabi’a mai kyau da kuma fatan alheri.
Ya ƙara da cewa rasuwar malamin babban rashi ne ga iyalansa, mabiya cocinsa, Kiristoci baki ɗaya da kuma Najeriya, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke buƙatar shugabanni masu haɗa kan al’umma da kira zuwa zaman lafiya da adalci.
A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana Rev. Okoye a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin Kiristoci a Najeriya, wanda hidimarsa ta zarce bambancin mazhabobi.
Ya ce marigayin ya kasance mai yaɗa gaskiya, zaman lafiya, adalci da sulhu, tare da ba da gudummawa wajen tarbiyyar shugabanni masu nagarta.
Adebayo ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, mambobin All Christians Fellowship Mission, Christian Association of Nigeria (CAN), Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) da kuma Kiristoci a faɗin duniya.
Dukansu sun yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama tare da bai wa iyalansa da mabiyansa juriyar wannan babban rashi.
