Fitaccen mawaƙin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa matarsa, Chioma Adeleke, ita ce ke kula da harkokin kuɗinsa, yana mai kiranta da “mai tsara rayuwata” (life coordinator).
A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga Davido yana kiran Chioma bayan ya kasa shiga asusun bankinsa domin aika wa mataimakinsa, Lati, kuɗi.
A yayin wayar, Davido ya roƙi Chioma da ta aika wa Lati dala 4,000 a madadinsa, yana mai bayyana cewa matsalar shiga asusun ta samo asali ne daga matsalar sabis.
Bayan kiran, wani mai shirya shirye-shiryensa ya tambaye shi ko matarsa ce ke kula da kuɗinsa.
Da yake amsawa, Davido ya tabbatar da hakan, yana mai cewa shi mutum ne mai yawan kashe kuɗi ba tare da ƙididdiga ba.
Ya ce:
“Eh mana. Ni mutum ne mai yawan kashe kuɗi. Ita ce ke tsara komai, ita ce mai kula da rayuwata.”
Kalaman na Davido sun jawo martani daga masoya da masu bibiyar harkokin nishaɗi, inda da dama suka yaba da irin amincewa da haɗin kai da ke tsakaninsa da matarsa.
