Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta tabbatar da cewa akalla ‘yan Najeriya 1,100 ne suka iso jihar Kano ta hanyar mota daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar.
Hukumar ta ce an tura jami’ai daga hukumomin tarayya da na jiha domin tantance, shawarwari da kuma taimakawa wajen sake shigar da su cikin iyalansu cikin aminci.
Kwamandan Makarantar Horas da Shige da Fice da ke Kano, Anthony Akuneme, ya bayyana cewa ana gudanar da tantancewar ta amfani da tsarin MIDAS a cibiyar MAKIA kafin daga bisani a kai su cibiyar ITS domin cikakken rajista, shawarwarin lafiya da tallafin sake haɗuwa da iyalai.
Ya ce dukkan hukumomin da abin ya shafa suna aiki tare don tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin tsari ba tare da tangarda ba.
Rahotanni sun nuna cewa Agadez na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ‘yan Afirka ke bi wajen neman hanyar shiga Turai, sai dai dokokin da Nijar ta kafa kan safarar mutane da kuma rikice-rikicen tsaro a yankin Sahel sun rage yawan masu wucewa.
Hukumar IOM ta bayyana cewa ‘yan Najeriya na daga cikin manyan ƙasashen da ake yawan dawo da ‘yan ƙasarsu daga yankin, musamman matasa da suka makale a hanya yayin ƙoƙarin tsallaka zuwa Turai.
