Gwamnatin Togo ta sanar da sabon tsarin da zai bai wa dukkan ‘yan kasashen Afirka damar shiga kasar ba tare da neman visa ba domin zaman kwanaki 30.
Sanarwar ta fito ne daga Ma’aikatar Tsaro ta kasar ranar Talata, inda ta bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin bunkasa hadin kai da saukaka zirga-zirga tsakanin kasashen Afirka.
A karkashin tsarin, duk wani dan kasar Afirka mai ingantaccen fasfo zai iya shiga Togo ba tare da visa ba muddin zamansa bai haura kwanaki 30 ba.
“Togo ta sake nuna kudirinta na karfafa hadin kan Afirka ta hanyar bude kofarta ga ‘yan nahiyar,” sanarwar ta bayyana.
Sai dai gwamnati ta ce matafiya dole ne su cike bayanan tafiya ta yanar gizo kafin awa 24 da isowarsu domin samun takardar amincewar shiga kasar.
Mahukuntan Togo sun ce sabon tsarin zai taimaka wajen karfafa alaka ta diflomasiyya, kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasashen Afirka.
Wannan mataki ya sanya Togo cikin jerin kasashen Afirka da suka rungumi tsarin shiga kasa ba tare da visa ba domin karfafa hadin kai a nahiyar.
