Lauya kuma jigo a jam’iyyar APC, Ademola Okeowo, ya janye daga takarar kujerar mazabar Ijebu North Constituency I ta Majalisar Dokokin Jihar Ogun domin mara wa dan takarar hadin kai na jam’iyyar, Olatunbosun Ipaye baya.
Okeowo ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ganawa da ‘ya’yan jam’iyya da manema labarai a sakatariyar APC ta karamar hukumar Ijebu North da ke Ijebu Igbo.
Ya ce tun farko ya shiga takarar ne saboda imaninsa cewa shugabanci dole ne ya kasance bisa hidima, gaskiya, kwarewa da kaunar jama’a, amma ya yanke shawarar janye takararsa domin tabbatar da hadin kan jam’iyyar bayan tattaunawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki.
“A koyaushe na yi imani cewa shugabanci ya kamata ya kasance bisa hidima, gaskiya da kwarewa. Wannan ne ya sa na shiga takarar domin wakiltar al’ummar Ijebu-Igbo,” in ji shi.
Ya kara da cewa irin goyon bayan da ya samu daga jama’a da magoya baya ya nuna cewa tafiyarsu ta zama wata babbar karfi mai cike da fata ga mutane da dama.
Sai dai ya ce bayan tuntubar shugabannin jam’iyya da dattawa, ya yanke shawarar janye takararsa ba tare da wani sharadi ba domin mara wa dan takarar hadin kai baya.
“Ba saboda tsoro ko rashin kwarewa na janye ba, amma domin hadin kai da ci gaban jam’iyya,” ya bayyana.
Okeowo ya sanar da cewa ya hade dukkan tsarinsa na siyasa da na dan takarar hadin kai tare da kira ga magoya bayansa da su mara wa APC baya a zaben da ke tafe.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban APC na karamar hukumar Ijebu North, Alhaji Adesegun Adenola, ya yabawa Okeowo bisa amincewarsa da matsayar jam’iyyar.
Adenola ya ce mutum 14 ne suka nuna sha’awar takarar kujerar, amma daga baya aka rage su zuwa mutum hudu, inda biyu daga cikinsu suka janye domin mara wa tsarin hadin kai baya kafin zaben fidda gwani da za agudanar.
