Iyalan wani matashi mai shekara 18 kuma ɗan takarar UTME, Kingsley Akunemeihe, sun roƙi fitaccen ɗan kasuwa Tony Elumelu da ya yafe masa bayan an kama shi kan wallafa labarin ƙarya a kafafen sada zumunta.
A cikin wani bidiyon roƙo da ‘yar uwarsa Ngozi Akunemeihe ta wallafa a Instagram ranar Lahadi, ta ce an kama ɗan uwanta ne bayan ya wallafa rubutu a shafin X (Twitter) da ke ikirarin cewa Elumelu ya rabu da matarsa Awele.
Ta bayyana cewa an kama shi ne a ranar 18 ga Afrilu, lokacin da yake dawowa gida bayan rubuta jarrabawar JAMB, kuma tun daga lokacin yana tsare.
“An kama ɗan uwana mai shekara 18, Kingsley Chinanu Akunemeihe, bayan ya fito daga jarrabawar JAMB. Har yanzu ba ya gida,” in ji ta.
Ngozi ta ce matashin bai ƙirƙiri labarin da kansa ba, sai dai ya kwafa shi daga wani shafi ya wallafa.
“Ya ce ya ɗauko labarin ne daga wani mutum ya wallafa. Daga baya aka sanar da shi cewa labarin ƙarya ne kuma ya yi illa,” ta bayyana.
Ta ƙara da cewa daga bisani ya gane kuskurensa, ya goge sakon tare da yin nadama a shafinsa.
“Ya fahimci kuskure kuma ya nemi gafara. Har yanzu sakon neman afuwar yana shafinsa,” in ji ta.
Duk da hakan, ta ce an kama shi bayan kusan kwanaki goma kuma yana tsare a sashen binciken manyan laifuka (SCID).
A cikin roƙon ta, ta bukaci Elumelu da ya yi la’akari da shekarunsa ya yafe masa.
“Don Allah ka yafe masa. Yaro ne mai shekara 18 kawai. Na san zai iya yin kuskure saboda rashin kwarewa,” ta roƙi.
Ta ce matakin da aka dauka ya riga ya zama darasi a gare shi kuma ya riga ya nuna nadama.
“Ya riga ya gane kuskurensa kuma ya nemi gafara. Ina roƙon a janye ƙorafin domin ya koma gida,” ta kara da cewa.
A baya, kamfanin UBA da Tony Elumelu ke jagoranta ya karyata labarin, yana mai cewa ƙarya ce kuma an yi shi ne domin bata suna.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa an sanar da hukumomin tsaro kuma an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin.
Lamarin ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta kan ‘yancin faɗin albarkacin baki, dokokin batanci, da kuma rawar da jami’an tsaro ke takawa a rikice-rikicen intanet.
