Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta tabbatar da faruwar rikicin ƙungiyoyin asiri (cult clash) a birnin Abeokuta da ya yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Oluseyi Babaseyi, ya fitar, ya ce jami’an sashen Oke Itoku sun fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
Rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:45 na rana a yankin Wasimi Ake Road, kusa da Centenary Hall da Lotus Bank, zuwa hanyar Ijemo Agbadu.
Rundunar ‘yan sandan ta jaddada cewa lamarin ba shi da alaƙa da wani taron siyasa ko taron jama’a a yankin.
“Wannan rikici bai faru a fadar Ake ba, kuma ba shi da alaƙa da taron Yayi Progressive Movement da aka gudanar a Ake Palace,” in ji sanarwar.
Binciken farko ya nuna cewa wasu ƙungiyoyin asiri masu adawa da juna sun shiga harbin bindiga kafin su tsere, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Jami’an ‘yan sanda da suka isa wajen sun tarar da wanda ya jikkata mai suna “Stone” kwance cikin jini sakamakon harbin bindiga.
An garzaya da shi asibitin jihar da ke Ijaiye, Abeokuta tare da taimakon hukumar agajin gaggawa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Daga baya aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa domin gudanar da binciken gawar (autopsy).
Rundunar ta ce an dawo da zaman lafiya a yankin, tare da ƙarin jami’an tsaro domin hana sake aukuwar irin haka.
“Mun fara farautar wadanda suka aikata laifin tare da bin sahihan bayanai domin cafke su da gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji rundunar.
‘Yan sanda sun kuma shawarci jama’a da su kasance cikin kwanciyar hankali amma su kasance cikin shiri, tare da bayar da bayanai da za su taimaka wajen bincike.
