Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Sokoto ta ce ta samu gagarumar nasara a yaki da ‘yan bindiga, inda ta dakile hare-haren da aka shirya kai wa wasu kauyuka tare da kwato harsasai 167 a sassan jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Hassan Shaffa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Sokoto.
Ya ce rundunar na ci gaba da daukar matakai na musamman domin dakile dukkan nau’o’in laifuka a jihar.
Dakile harin Sabon Birni
A cewarsa, a ranar 8 ga Afrilu, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji da ‘yan sa-kai sun dakile harin ‘yan bindiga a kauyukan Kwarangamba da Gaya da ke karamar hukumar Sabon Birni.
Ya ce an yi musayar wuta, inda hakan ya tilasta ‘yan bindigar guduwa da raunuka.
“A lokacin bin sawu, sun bar buhu dauke da harsasai 167,” in ji shi.
Samamen maboyar masu laifi
A ranar 15 ga Afrilu kuma, an gudanar da samame a Tambuwal, Kware da Goronyo, inda aka kama mutum uku da ake zargi tare da kwato bindiga ta gida, AK-47 magazine, da wasu abubuwa da ake zargin tabar wiwi ne.
Kame mai taimaka wa ‘yan bindiga
Haka kuma an kama wani Aminu Meroba da ake zargi da taimaka wa ‘yan bindiga wajen safarar shanu da kudaden haram.
Kalubalen tsaro
Kwamishinan ya amince da kalubalen tsaro a wasu yankuna kamar Achida da kewaye, amma ya ce an kara tura jami’an tsaro domin shawo kan matsalar.
“Muna kara karfafa tsaro da hadin gwiwa da al’umma,” in ji shi.
