Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sanya ranar Litinin domin tantance Hon. Murtala Sule Garo, bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika sunansa a matsayin wanda zai zama sabon Mataimakin Gwamna.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da kakakin Majalisar, Kamaludden Shawai, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Majalisar ta riga ta karɓi takardar nadin daga Gwamnan domin gudanar da cikakken tantancewa da amincewa.
An bayyana cewa za a gudanar da tantancewar ne a harabar Majalisar a ranar Litinin mai zuwa, inda za a duba cancanta da kwarewar wanda aka zaba.
Gwamna Abba Yusuf ya aika da sunan Murtala Garo ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi gyara), wanda ke bai wa Gwamna damar nada sabon Mataimakin Gwamna idan gurbi ya samu.
Wannan gurbi ya biyo bayan murabus din tsohon Mataimakin Gwamna, Abdussalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, 2026.
