Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai gayyaci Murtala Sule Garo domin tantancewa don naɗa shi a matsayin mataimakin Gwamna.
Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ne ya sanar da kafa kwamitin jim kaɗan bayan karanta wasikar da Gwamna ya aikewa majalisar ta nadin Murtala Garo.
Kwamitin bisa jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello Ɓutu-Ɓutu, a nasa ran zai gabatar da rahoton sa a gaban majalisar a ranar Litinin mai zuwa.