Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya amince da bai wa ma’aikatan gwamnati hutun rana guda a kowane mako tare da biyan su ₦10,000 a matsayin kudin sufuri na tsawon watanni uku, daga watan Afrilu 2026.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikata na jihar, Kehinde Onasanya, ya fitar a ranar Alhamis.
Onasanya ya ce an dauki wannan mataki ne domin rage radadin karin farashin mai da kuma tashin kudin rayuwa da sufuri da ke addabar ma’aikata.
Ya ce, “Domin taimakawa ma’aikatan jihar Ogun sakamakon karin farashin mai da kuma tsadar rayuwa, Gwamna Dapo Abiodun ya amince da hutun rana guda a mako ga ma’aikata.
“Haka kuma, za a rika biyan ₦10,000 a matsayin kudin sufuri na musamman na tsawon watanni uku daga watan Afrilu 2026.”
Ya kara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen saukaka rayuwar ma’aikata tare da kara inganta aikin su.
Sai dai ya bayyana cewa ma’aikatan da ke gudanar da ayyuka masu muhimmanci kamar:
likitoci da ma’aikatan lafiya
ma’aikatan kotu
malamai
jami’an tsaro
shugabannin sassa
ba za su amfana da hutun ranar mako ba, amma za su karbi kudin sufuri.
Ya kuma ce shugabannin ma’aikatu da hukumomi ne za su tsara ranar hutun domin tabbatar da cewa ayyukan gwamnati ba su tsaya ba.
Onasanya ya yaba wa gwamnan bisa wannan mataki, yana mai cewa lokaci ya yi daidai, tare da kira ga ma’aikata da su kara himma da jajircewa a aikinsu.
