Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da yin abin da zai iya haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya yi zargin cewa INEC ta bai wa Nafiu Bala Gombe lambar shiga tsarin hukumar (access code), duk da cewa, a cewarsa, Sanata David Mark ne shugaban jam’iyyar ADC da hukumar ta amince da shi.
Atiku ya ce idan har wannan zargi ya tabbata, hakan ya saɓa wa dokokin zaɓe da kuma ƙa’idojin INEC, kuma zai iya jefa jam’iyyar cikin sabon rikici gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya jaddada cewa bisa dokar zaɓe da kundin tsarin mulkin Najeriya, jam’iyya na da damar gabatar da sahihin ɗan takara guda ɗaya kacal ga kowane muƙami, bayan gudanar da zaɓen fidda gwani da INEC ta sa ido a kai.
Atiku ya kuma yi iƙirarin cewa duk wata takara da aka gabatar ba tare da amincewar shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark ba, ba ta da inganci a doka.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya buƙaci INEC da ta guji duk wani mataki da zai iya haddasa rikici a cikin jam’iyyun siyasa, yana mai cewa hukumar ta kamata ta kasance mai nuna adalci da bin doka.
Sai dai, zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen da Atiku Abubakar ya yi ba.
