Masu ruwa da tsaki daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu sun fara tattaunawa kan samar da sabon tsari da zai ba kamfanoni da masu kirkire-kirkire a Najeriya damar amfani da hakkokin mallakar fasaha (Intellectual Property – IP) a matsayin jinginar samun rancen kuɗi.
An gudanar da taron ne a Abuja karkashin jagorancin The New Practice (TNP) tare da haɗin gwiwar World Intellectual Property Organisation (WIPO), a wani ɓangare na shirin Investment in Digital and Creative Enterprises (iDICE).
Shirin iDICE na samun goyon bayan Bankin Masana’antu (BOI) a madadin Gwamnatin Tarayya, tare da tallafin Bankin Raya Afirka (AfDB), Agence Française de Développement (AFD) da Islamic Development Bank (IsDB).
Mahalarta taron sun tattauna hanyoyin da za a ba wa haƙƙin mallakar fasaha kamar copyright, trademark da patent darajar da za ta ba su damar zama kadarorin da bankuna za su amince da su wajen bayar da rance.
Sun bayyana cewa duk da muhimmancin waɗannan kadarori ga kamfanonin fasaha da masana’antun kirkire-kirkire, har yanzu tsarin bayar da rance a Najeriya bai cika amincewa da su a matsayin jingina ba.
Abokin hulɗa a TNP, Samuel Esuga, ya ce akwai buƙatar samar da ingantaccen tsarin tantance darajar hakkokin mallakar fasaha da kuma ƙarfafa dokokin kare su domin su zama abin amincewa wajen samun kuɗaɗen zuba jari.
Shi ma shugaban kwamitin fasaha na shirin iDICE, Dr. Magnus Abeng, ya ce sabon tsarin zai taimaka wa kamfanonin fasaha, masu kirkire-kirkire da ‘yan kasuwa samun damar rancen kuɗi ta hanyar amfani da kadarorin basirarsu.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana fatan cewa idan aka aiwatar da wannan tsari, zai ƙara jawo masu zuba jari, inganta samun kuɗaɗe ga sabbin kamfanoni da kuma bunƙasa tattalin arzikin fasaha da kirkire-kirkire a Najeriya.
