Hukumar Kula da Fansho ta Kasa (PenCom) ta bayyana cewa adadin kudaden fansho a Najeriya ya karu da kashi 51% cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ya tashi daga Naira tiriliyan 20.7 zuwa Naira tiriliyan 31.48.
Darakta Janar ta PenCom, Omolola Oloworaran, ta ce wannan ci gaba ya samo asali ne daga karuwar amincewar jama’a da tsarin fansho na Najeriya, tare da karin masu shiga shirin.
Ta kuma bayyana cewa sama da sabbin mutum 938,000 sun shiga tsarin fansho cikin shekaru biyu, yayin da gwamnatin tarayya ta amince da karin Naira 32,000 ga wasu masu karbar fansho da suka cancanta bayan aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
Haka kuma, PenCom ta ce kudaden fansho da ake biya duk wata sun karu daga Naira biliyan 12.2 zuwa Naira biliyan 14.9, yayin da sama da masu karbar fansho 195,000 suka riga suka amfana da sabon karin.
