Hukumar Kula da Bin Doka ta Jihar Oyo (OYRLEA) ta kara tsaurara matakan yaki da kiwon dabbobi ba bisa ka’ida ba, inda ta kwace wasu dabbobi da aka samu suna kiwo a haramtaccen wuri a yankin Apata Olomo da ke kan titin Ado-Awaye a karamar hukumar Iseyin.
Shugabar hukumar, Mai Shari’a Aderonke Aderemi mai ritaya, ta ce an gudanar da aikin ne bayan manoma sun kai korafin cewa wasu dabbobin makiyaya sun lalata gonakinsu tare da cin amfanin gona, lamarin da ya jawo musu asara mai yawa.
A cewarta, tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Francis Ojoomo tare da sauran jami’an hukumar sun kai ziyara yankin domin bincike, inda suka tabbatar da korafe-korafen da aka gabatar.
Binciken ya nuna cewa an samu dabbobi suna kiwo a fili ba tare da bin dokokin kula da kiwo da dabbobi na jihar ba, lamarin da ya sa jami’ai suka kwace wasu daga cikin dabbobin.
Hukumar ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da bin doka, kare manoma da gonakinsu, tare da tabbatar da cewa masu kiwo suna bin ka’idojin da gwamnati ta shimfida.
Jihar Oyo na daga cikin jihohin da suka kafa dokoki da matakan dakile kiwo a fili domin rage rikice-rikicen manoma da makiyaya, kare harkokin noma da kuma inganta samar da abinci.
