Hukumar Kula da Harkokin Magunguna ta Kasa (PCN) ta cafke mutane biyar da ake zargi da karya hatimin da aka sanya wa wasu shagunan sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu a Jihar Kano.
Daraktan Sashen Sa-ido na PCN, Dakta Suleiman Chiroma, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce an kama mutanen ne yayin wani samame da ake ci gaba da yi a kasuwannin Dalan Gyada da Kurmi, wuraren da aka haramta sayar da magunguna.
A cewarsa, mutum uku daga cikin wadanda aka kama sun karya hatimin da hukumar ta sanya wa shagunansu a baya, yayin da aka kama wasu biyu suna gudanar da sana’ar sayar da magunguna ba tare da izini ba.
Chiroma ya bayyana cewa karya hatimin gwamnati ko sake bude shagunan da aka rufe babban laifi ne karkashin Dokar Kafa Hukumar PCN ta shekarar 2022.
Ya ce tuni aka tsare wadanda ake zargin kuma za a gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Tarayya domin fuskantar hukunci, yayin da lauyoyin hukumar ke shirye domin tabbatar da an gudanar da shari’ar yadda ya kamata.
Daraktan ya sake jaddada cewa kasuwannin Dalan Gyada da Kurmi har yanzu wurare ne da aka haramta sayar da magunguna, yana mai gargadin jama’a da su guji sayen magunguna daga masu sana’ar da ba su da lasisi.
Ya kuma bukaci al’umma su rika sayen magunguna ne kawai daga cibiyoyi da shagunan da PCN ta amince da su domin tabbatar da inganci da amincin magungunan da suke amfani da su.
Chiroma ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen dakile harkokin sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba tare da tsaftace tsarin rabon magunguna a fadin Najeriya.
