Gwamnatin Tarayya ta Najeriya da gwamnatin Habasha sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da za ta bai wa fursunonin Najeriya sama da 100 da ke zaman gidan yari a Habasha damar komawa gida domin ci gaba da zaman hukuncinsu.
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana hakan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tare da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, a birnin Addis Ababa na Habasha.
Ta ce yarjejeniyar ta shafi mayar da fursunonin Najeriya da ke gidajen yarin Kaliti da Aba Samuel zuwa Najeriya domin su ci gaba da zaman hukuncin da aka yanke musu a cibiyoyin gyaran hali na kasar.
A cewarta, yarjejeniyar ta samo asali ne daga ka’idojin jin kai, adalci da kuma kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu, tare da nuna kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare muradun ’yan Najeriya da ke kasashen waje.
Ministar ta bayyana cewa mutane hudu daga cikin fursunonin Najeriya sun rasu yayin da ake ci gaba da tattaunawa da tantancewar doka kafin cimma wannan yarjejeniya, lamarin da ya kara nuna muhimmancin gaggauta aiwatar da shirin.
Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da ke rayuwa ko tafiye-tafiye a kasashen waje da su mutunta dokokin kasashen da suke zaune domin kare martabar Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya na kokarin dawo da kusan ’yan Najeriya 300 da ke zaman gidan yari a Habasha, sakamakon damuwa kan matsin rayuwa da ake fuskanta a wasu gidajen yarin kasar.
Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta bai wa fursunonin da abin ya shafa damar kammala sauran wa’adin hukuncinsu a cibiyoyin gyaran hali na Najeriya, yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin tabbatar da mutuncinsu da hakkokinsu bisa dokokin kasa da kasa. :::
