Mai taimakawa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wato Paul Ibe, ya bukaci Hukumar Tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro da su gayyaci mai rajin ‘Yoruba Nation, Sunday Adeyemo (Sunday Igboho), domin yi masa tambayoyi kan ikirarin da ya yi game da sace dalibai da malamai a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
Ibe ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) a ranar Alhamis, inda ya ce idan Igboho yana da bayanai kan wadanda ke da hannu a sace-sacen, ya kamata a yi amfani da shi wajen taimakawa aikin ceto wadanda aka sace.
Wannan kira na zuwa ne bayan Ikirarin da Igboho ya yi a wata ganawa da kungiyar daliban Najeriya (NANS), inda ya ce ya san ‘yan siyasar da ke da hannu a sace daliban, tare da gargadin cewa zai tona musu asiri idan lamarin ya ci gaba.
A cewar Ibe, dole ne hukumomin tsaro su yi amfani da duk wata hanya da za ta taimaka wajen ganin an kubutar da daliban da aka sace cikin gaggawa.
Ya ce:
“Tun da Sunday Igboho ya ce ya san wadanda ke da hannu a sace daliban Oriire, ina ganin DSS da sauran hukumomin tsaro su gayyace shi ya bayyana sunayen ga hukumomi.”
Ya kuma yi kira da gwamnati ta dauki duk matakan da suka dace domin ganin an kubutar da daliban.
Ibe ya kuma nuna damuwa kan rahoton sace fiye da dalibai 50 a Mussa, Jihar Borno, a ranar 15 ga Mayu, 2026, yana tambayar dalilin shiru da gwamnati ta yi kan lamarin.
Ya ce dole ne a rika daukar dukkan ‘yan Najeriya da muhimmanci iri daya wajen magance matsalar tsaro, ba tare da nuna bambanci ba.
Haka kuma ya bukaci a kara matakan tsaro na kariya, ciki har da tura masu gadin dazuka (forest guards) a jihohin da ke fuskantar barazana, domin hana aukuwar hare-hare kafin su faru.
