Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja University of Abuja Teaching Hospital, Prof. Thairu Yunusa, ya jaddada aniyar asibitin wajen ci gaba da bayar da ingantaccen kulawa ga marasa lafiya cikin tausayi da kwarewa, bayan nasarar kula da wata mata mai shekaru 26 da ta warke daga cutar sankarar mahaifa.
An gudanar da wani biki a asibitin da ke Gwagwalada domin karrama matar mai suna Mercy Moses, wacce ta samu cikakkiyar kulawa har ta warke daga cutar.
Prof. Yunusa ya bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga asibitin, yana mai cewa hakan ya nuna karuwar kwarewar ma’aikatan lafiya a Najeriya wajen kula da cututtuka masu tsanani.
Ya ce nasarar ta samo asali ne daga hadin gwiwar likitoci, ma’aikatan jinya, masu aikin rediyo da sauran ma’aikata a sassa daban-daban na asibitin.
A cewarsa, Mercy ta rika zuwa asibitoci daban-daban kafin ta isa UATH, inda aka hada gwiwar kwararru suka yi nasarar kula da ita har ta warke.
Likitan mata, Dr. Ishaq Lawal, ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba a fannin kula da sankarar mahaifa, inda ya ce an hada magunguna kamar chemotherapy da radiotherapy kafin a yi mata tiyata mai zurfi.
Ya kuma ce ana shirin kafa Asusun Tallafawa Marasa Karfi na Ciwon Sankara domin taimaka wa marasa galihu wajen samun cikakkiyar kulawa.
Wannan nasara na kara nuna cewa asibitocin koyarwa a Najeriya na samun ci gaba wajen kula da cututtuka masu sarkakiya ta hanyar kwarewa da aiki tare.
