Hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps reshen jihar Kano ta bayyana shirin tura jami’ai 3,250 domin tabbatar da tsaro mai inganci yayin bukukuwan Sallar Eid-el-Kabir a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an kammala dukkan shirye-shirye domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan sallah a fadin jihar.
Kwamandan hukumar a jihar, Commandant Mohammed Hassan Agalama, ne ya amince da tura jami’an a sassa daban-daban na Kano domin kula da tsaro.
Hukumar ta ce za a fi mayar da hankali kan filayen sallar Eid, wuraren shakatawa, da sauran wuraren taruwar jama’a a lokacin bukukuwan.
Haka kuma za a kara tsaurara tsaro a muhimman wuraren gwamnati da kayayyakin more rayuwa, yayin da tawagar gaggawa ta hukumar za ta ci gaba da sintiri da sa ido.
NSCDC ta kuma yi gargadi ga bata-gari da su guji tada fitina, tana mai cewa za ta dauki mataki kan duk wanda ya karya doka ko ya tayar da hankalin jama’a a lokacin bukukuwan.
