Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta nada tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sanata Sam Egwu, a matsayin shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da ‘yan majalisar wakilai gabanin babban zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakatarenta na kasa, Ikenna Morgan Enekweizu, ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce za a kaddamar da kwamitin mai mambobi 17 da karfe 4 na yammacin ranar Talata, 19 ga Mayu, 2026.
Egwu, wanda ya taba zama gwamna na wa’adi biyu tare da wakiltar jama’a a majalisar dokoki, zai jagoranci kwamitin da zai tantance duk masu neman mukaman siyasa a karkashin jam’iyyar NDC.
Jam’iyyar ta kuma nada babban mai ba ta shawara kan harkokin shari’a, Reuben Egwuaba, a matsayin sakataren kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Babatunde Ali a matsayin mataimakin shugaba, Buba Galadima, Mohammed Takori, Daniel Onifade, Ikeddy Isiguzo, Wole Adedayo, Dr Osusu Osusu, Chief Asukewe Ikoawaji, Prof. Udenta Udenta, Frederick E. Owotorufa, Hannatu Tanko, Dogo Shammar, Sir Henry Obaze, Clement Agiagie da Fatima Abba.
Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa an zabo mambobin kwamitin ne daga cikin shugabannin jam’iyya, kwararru da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa domin tabbatar da sahihanci da gaskiya wajen tantance ‘yan takara.
Matakin na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke kara shirye-shiryen babban zaben 2027, inda a baya-bayan nan ta fara amfani da tsarin hadin kai wajen zabo wasu ‘yan takara domin kauce wa rikicin cikin gida da kuma karfafa hadin kan jam’iyyar.
