Shahararren mai wallafa labarai kuma ɗan kasuwa a harkar kafofin watsa labarai, Dele Momodu, ya soki abin da ya kira “cin zarafin” tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, yana mai tunatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, ya taɓa zama mataimakinsa a zaɓen baya.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, Momodu ya ce abin takaici ne yadda ake mu’amala da Atiku duk da cewa ya taɓa bai wa Obi tikitin mataimakin shugaban ƙasa a 2019.
“Abin baƙin ciki ne matuƙa ganin yadda ake cin zarafin mutumin da ya ba PETER OBI tikitin Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yana ganin wasu “fake OBIDIENTS” da kuma masu tayar da rikici ne ke haddasa wannan yanayi.
Daga baya a cikin tattaunawa ta X Space, Momodu ya yi tsokaci kan zaɓen 2023, tsarin rarrabuwar ƙuri’u a yankuna, da kuma siyasar adawa a Najeriya.
Ya kuma yi tambaya kan ikirarin cewa Peter Obi ya lashe zaɓen, yana mai cewa sakamakon zaɓe ya nuna yadda yankuna ke ba da ƙuri’u ga ‘yan takara daban-daban.
“Ka ce Obi ya ci zaɓe amma ba a ba shi mulki ba. A 2023, Peter Obi ya samu kusan kashi 100 na ƙuri’u a yankinsa,” in ji shi.
Momodu ya kuma ce yana da wuya a samu goyon bayan ƙasa baki ɗaya a siyasar Najeriya, inda ya ce:
“Mutanen Arewa ba za su mutu saboda wani ɗan takarar Kudu ba.”
Wannan magana ta jawo ce-ce-ku-ce daga wasu masu sauraro da suka ce kalmar na iya rage darajar wasu ‘yan siyasa.
Yayin da yake kare Atiku, Momodu ya bayyana shi a matsayin ɗan siyasa mai ƙwarewa da jajircewa, yana mai cewa ya zo na biyu a zaɓen baya.
Ya kuma ce zaɓe na gaba zai iya zama mai matuƙar muhimmanci ga Atiku.
“Wannan zai iya zama na ƙarshe; idan ya fadi fitar takara, to hakan na iya zama ƙarshen,” in ji shi.
Momodu ya kuma yi kira da a guji cin mutuncin shugabanni a kafafen sada zumunta, yana mai cewa ya kamata a riƙa nuna ladabi a siyasa.
“Bari mu guji halin ‘yan daba… cin mutuncin mutane yana nuna halin mutum,” in ji shi.
Ya ƙara jaddada cewa zai ci gaba da goyon bayan Atiku, yana mai kiran kansa “na ƙarshe da ya rage a fagen.”
