Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Kudu, Sunday Katung, ya ayyana kudirinsa na sake tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa a zaben shekarar 2027.
Katung ya kuma bayyana goyon bayansa ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani domin neman wa’adi na biyu.
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar APC daga yankinsa, wanda aka gudanar a birnin Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Midat Joseph, ya fitar, Katung ya ce matakin nasa ya samo asali ne daga bukatar ci gaba da ayyukan da ya fara da kuma kammala muhimman ayyuka a yankin Kudancin Kaduna.
“Ina neman wa’adi na biyu domin kara gina nasarorin da muka samu, kammala ayyukan da muka fara, da kuma ci gaba da wakiltar al’ummarmu yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya kuma danganta kudirinsa da manufofin gwamnatin tarayya da na jihar Kaduna, yana mai cewa shirin “Renewed Hope” na gwamnatin Tinubu da kuma tsare-tsaren ci gaban gwamnatin Uba Sani na bukatar gogaggun ‘yan majalisa domin tabbatar da aiwatar da su a matakin kasa da kasa.
Katung ya bukaci ‘yan jam’iyya da su kara zage damtse wajen shirye-shiryen zaben 2027, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai da karfafa jam’iyyar APC a yankin.
“Aikin da ke gabanmu na bukatar hadin kai, jajircewa da tsari mai kyau. Dole ne Kudancin Kaduna ya ci gaba da kasancewa tare da APC domin ci gaba da samun ci gaba,” ya kara da cewa.
Sanatan ya kuma tabbatar da kudirinsa na gudanar da shugabanci mai hada kai da ci gaba mai dorewa a dukkan kananan hukumomi takwas da ke yankin Kaduna ta Kudu.
Katung, wanda ke wa’adinsa na farko a majalisar dattawa, ya taka rawar gani wajen aiwatar da dokoki da kuma ayyukan raya mazabu da suka shafi ababen more rayuwa da walwalar jama’a.
