Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi a fadin Najeriya da su fita domin neman ganin jinjirin watan Zulki’ida 1447AH.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Harkokin Addini na Masarautar Sakkwato, Sambo Junaidu, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga Shawwal 1447AH, ita ce aka ware domin neman ganin jinjirin watan.
An kuma bukaci duk wanda ya ga jinjirin da ya sanar da shugaban unguwa ko na ƙauye mafi kusa domin a isar da bayanin ga Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta jaddada muhimmancin wannan aiki wajen tantance farkon sabon watan Musulunci, tare da kira ga al’umma da su bada hadin kai wajen aiwatar da shi.
