Hukumar ‘Niger State Police Command’ ta kama mutane 16 da ake zargi da tayar da tarzoma a birnin Minna, babban birnin jihar.
An yi kamun ne yayin wani aikin farmaki daga gida zuwa gida da ‘yan sanda suka gudanar da misalin karfe 2 na dare.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin suna dauke da wuka, sanda, aski, da gatari.
Daga cikin wadanda aka kama akwai:
Najeem Yakubu (Kuta Road)
Zakari Hussaini (Kuta Road)
Idris Saidu (Sabongari)
Naziru Kabiru (Angwan-Sarki)
Shehu Sulaiman (Ogbomosho Road)
Anas Abubakar (Kotun-Bola)
da sauran mutane da dama.
Hukumar ta ce wadanda aka kama suna ƙarƙashin bincike a halin yanzu, sannan za a mika su zuwa Criminal Investigation Department (CID) na jihar domin ci gaba da bincike.
‘Yan sanda sun jaddada cewa za a ci gaba da daukar matakai don tabbatar da tsaro ga mazauna jihar.
