Fitacciyar jarumar Nollywood, Shan George, ta bayyana ra’ayinta kan shugabancin Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce ya fi nuna kwarewa da tasiri a lokacin da yake gwamnan jihar Legas.
A wata hira da ta yi, Shan George ta nuna cewa ba ta ganin irin hazaka da kwazon da ake danganta da shugaban a yanzu kamar yadda yake a baya.
Ta tuna yadda Tinubu ya gudanar da mulki a Legas, inda ta ce ya kawo manyan sauye-sauye duk da rikicin siyasa da ya samu da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
“Ina tuna lokacin da Tinubu yake gwamnan Legas, ya yi abubuwa da dama da suka canza birnin. Ya gina MM2, ya fadada hanyoyi, ya rage ‘yan daba a titi, ya kuma kafa LASTMA,” in ji ta.
Sai dai ta ce shugaban na yanzu ya sa ta cikin tunani, tana tambayar inda tsohon Tinubu mai fafutuka ya tafi.
A cewarta, shekaru na iya zama daya daga cikin dalilan da suka kawo wannan sauyi, tana mai cewa lokaci ya yi da shugaban zai yi murabus cikin mutunci.
“A ganina, shekaru ne suka yi tasiri. Ya kamata ya sauka da kansa yayin da har yanzu ana yaba masa,” ta kara da cewa.
Shan George ta kuma yi zargin cewa makusantan shugaban ba za su gaya masa gaskiya ba saboda amfanin da suke samu.
Duk da haka, ta jaddada cewa ba ta goyon bayan kowace jam’iyya, kuma ta bayyana kanta a matsayin ‘yar kasa mai fadin ra’ayinta cikin girmamawa.
