Shugaban Cocin Katolika, Pope Leo XVI, ya yi tattaunawa ta waya a ranar Juma’a da shugabannin ƙasashen Israel da Ukraine, inda suka tattauna kan rikice-rikicen da ke gudana da kuma bukatar samar da zaman lafiya.
Fadar Vatican ta bayyana cewa Paparoma ya yi magana da shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, da kuma shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, inda suka mayar da hankali kan halin da fararen hula ke ciki a yankunan da ake fama da yaki.
A cikin wata sanarwa, an ce Paparoma da Herzog sun jaddada bukatar sake bude hanyoyin tattaunawar diflomasiyya domin kawo karshen rikicin da ke gudana, tare da neman samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar ta kara da cewa tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan kare rayukan fararen hula da kuma tabbatar da mutunta dokokin kasa da kasa da na jin kai yayin rikici.
Wannan tattaunawa ta zo ne a lokacin da ake gudanar da bukukuwan addini daban-daban a duniya, inda Paparoma ke jagorantar makon ibadar Katolika na Holy Week gabanin Easter.
A gefe guda kuma, shugaban Isra’ila yana bikin Passover, yayin da shugaban Ukraine, wanda dan asalin Yahudawa ne, ke shirin bikin Easter na Orthodox da zai gudana a ranar 12 ga Afrilu.
A wata sanarwa daga ofishin Herzog, an ce sun fara tattaunawar ne da musayar gaisuwar bukukuwan addini kafin su tattauna kan rikicin da ya shafi Iran, ciki har da barazanar harba makamai masu linzami da kungiyoyin da ake zargi suna da alaka da kasar.
Haka kuma, sun tattauna kan halin tsaro a Lebanon, musamman yadda za a kare al’ummomin Kiristoci da ke zaune a yankunan kan iyaka.
