Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sace mutane 10 yayin da suke Sallar Asubahi a garin Bushe, na yankin Sabon Birni a jihar Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ya bayyana hakan a jiya Juma’a, yana mai cewa maharan sun kai farmaki a lokacin ibada tare da yin garkuwa da masallatan, ciki har da Limamin Masallacin garin. Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun dukufa wajen kubutar da wadanda aka sace.
