Kungiyar SERAP ta buƙaci dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa 19 da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta bayyana gabanin zaɓen 2027 da su fito fili su bayyana kadarorinsu da basussukansu, da na ma’auratansu, da kuma ’ya’yansu da ba su kai shekara 18 ba, inda ya dace.
SERAP ta kuma buƙaci ’yan takarar da su bayyana halastattun hanyoyin da suka samu manyan kadarorinsu, tare da yin watsi a fili da sayen ƙuri’a da rashawa a lokacin zaɓe.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙar buɗe wa ’yan takarar da aka sanya wa hannu ranar 8 ga Agusta, 2026, wadda mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar.
Daga cikin ’yan takarar da SERAP ta ambata akwai Shugaba Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi na NDC, Sandy Onor na PDP, Omoyele Sowore na AAC da Donald Duke na PRP.
Sauran sun haɗa da Okwori Ada Elizabeth Frederick, Chukwu Anita Zugwai, Rufai Adekunle Omoaje, Adenuga Sunday, Memeh Samuel, Nwanyanwu Daniel Danerechukwu, Okereke Sunday Chibuzor, Okereke Iken Esther, Abbas-Bin Aliyu, Dikwa Suleiman Mohammed, Adebayo Adewole Ebenezer, Seyi Makinde da Yusuf Kabiru.
SERAP ta ce ’yan takarar ya kamata su wuce abin da doka kawai ta buƙata, su rungumi ƙa’idojin gaskiya, riƙon amana da bayyana bayanai domin nuna wa ’yan Najeriya cewa harkokin kuɗaɗensu na iya jure binciken jama’a.
Kungiyar ta jaddada cewa mutanen da ke neman shugabancin ƙasar, wanda ke da iko kan dukiyar jama’a, albarkatun ƙasa, naɗe-naɗe da hukumomin tsaro, ya kamata su kasance a shirye su bayyana halin da kadarorinsu suke ciki kafin su nemi ƙuri’un ’yan Najeriya.
