Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya ƙaddamar da manhajar wayar salula mai suna SoworeNow a matsayin dandalin hukuma na magoya bayansa domin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Sowore ya sanar da hakan ne ta wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya ce manufar manhajar ita ce haɗa magoya baya tare da sauƙaƙa musu samun sahihan bayanan yaƙin neman zaɓensa.
Ya bayyana cewa ta hanyar manhajar, masu amfani za su riƙa samun sabbin bayanai daga yaƙin neman zaɓe, shiga gangamin siyasa, da kuma haɗa kai da sauran magoya bayan jam’iyyar AAC domin tallafa wa ƙudirinsa na sauyi.
Sowore ya ce, “Canji na gaskiya yana farawa ne da aiki, kuma aiki yana farawa da ku.”
