Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA) ta sanar da shirin cire tsofaffin kwale-kwale da ba su da ingancin tsaro daga aiki, tare da gyarawa da faɗaɗa tashoshin jiragen ruwa (jetties) a faɗin ƙasar domin rage yawan haɗurran ruwa.
Shugaban Hukumar NIWA, Barrister Mukhtar Shehu Shagari, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar duba ayyukan hukumar a ofishinta na yankin Lagos.
Shagari ya ce sabon kwamitin gudanarwar NIWA ya fara aikin tantance dukkan kayayyakin more rayuwa na hukumar a faɗin ƙasar domin gyara tsofaffin ofisoshi da tashoshin jiragen ruwa, tare da ƙara sabbin wuraren sauka da tashi na jiragen ruwa.
Ya bayyana cewa an ware kuɗi a kasafin kuɗin hukumar domin magance matsalolin gine-gine da kayayyakin aiki a dukkan ofisoshin NIWA.
A cewarsa, hukumar za ta ƙara yawan tashoshin jiragen ruwa musamman a jihar Lagos domin biyan buƙatar da ake da ita na sufurin ruwa.
Shagari ya kuma ce NIWA za ta fara cire dukkan kwale-kwale marasa inganci daga aiki tare da maye gurbinsu da sababbi masu ingancin tsaro.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta yi haɗin gwiwa da masu ƙera kwale-kwale na cikin gida da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta harkokin sufurin ruwa a Najeriya.
Dangane da tabbatar da doka, shugaban hukumar ya ce NIWA na aiki tare da rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin dakile ayyukan haramtattun tashoshin jiragen ruwa da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro.
Ya kuma yi kira ga masu zuba jari masu zaman kansu da su haɗa kai da NIWA wajen ayyukan haƙa hanyoyin ruwa, gina kayayyakin more rayuwa da bunƙasa harkokin sufurin ruwa.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan NIWA, Yusuf Gerie, ya ce ziyarar na da nufin gano matsalolin da ke hana ingantaccen aiki tare da samar da hanyoyin magance su.
Shi ma ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Shuɗi, Adegboyega Oyetola, bisa kafa kwamitin da zai inganta ayyukan NIWA da bunƙasa tattalin arzikin ruwa a Najeriya.
