Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa aikin injiniya ba wai gina tituna, gadoji da gine-gine kaɗai ba ne, har ila yau yana da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Yayin da yake buɗe taron shekara-shekara na Council for the Regulation of Engineering in Nigeria (COREN), Tinubu ya ce duk wata gazawa a aikin injiniya na iya haifar da asarar rayuka, lalacewar dukiyoyi da kuma asarar amincewar jama’a.
Ya jaddada cewa dokokin da ke kula da aikin injiniya ba hukunci ba ne, sai dai kariya ga rayuka, masu zuba jari da dukiyoyin ƙasa.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa na aiwatar da manyan ayyukan tituna a faɗin ƙasar nan, inda aka tsara su domin su ɗore na tsawon shekaru 50 zuwa 100, sabanin yadda wasu tituna a baya ba su kai shekaru biyar ba kafin su lalace.
A nasa jawabin, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya gargaɗi injiniyoyin da ke kula da ayyukan gine-gine da kada su bari ‘yan kwangila su rinjaye su wajen yanke shawarar fasaha. Ya ce kuskuren injiniya na iya jawo asarar rayuka, saboda haka COREN ta tabbatar da cewa ƙwararrun injiniyoyi kaɗai ke gudanar da aikin.
Shugaban COREN, Farfesa Sadiq Abubakar, ya ce hukumar ta ƙara ƙaimi wajen sa ido kan ayyukan gine-gine, amfani da tsarin dijital, da kuma ɗaukar matakan kariya kafin matsaloli su faru.
Shi ma shugaban Dangote Group, Aliko Dangote, ta bakin Babban Masanin Tattalin Arzikin kamfanin, Farfesa Hassan Mahmoud, ya ce ingantaccen tsarin aikin injiniya na ƙarfafa ci gaban masana’antu, jawo masu zuba jari, da kuma rage haɗarin rushewar ababen more rayuwa.
Masu ruwa da tsaki sun amince cewa ƙarfafa dokokin aikin injiniya, bin ƙa’idojin ƙwararru da hukunta masu karya doka za su taimaka wajen rage rushewar gine-gine da sauran matsalolin ababen more rayuwa a Najeriya.
