Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) na shirin tsawaita hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya zuwa kusan minti 30, domin gudanar da babban shirin nishadi irin na Super Bowl.
Rahotanni sun bayyana cewa tashoshin talabijin na BBC da ITV sun riga sun shirya don wannan sauyi, inda ake sa ran za a yi wasan kwaikwayo na kusan minti 11, sannan a ci gaba da sharhin masana na minti 15.
Sai dai dokokin ƙwallon ƙafa sun tanadi cewa hutun rabin lokaci bai kamata ya wuce minti 15 ba. Duk da haka, FIFA ta taɓa tsawaita hutun zuwa minti 25 a Gasar Cin Kofin Kungiyoyin Duniya da ta gabata.
An kuma bayyana cewa fitattun mawaka da masu nishaɗi da suka haɗa da Madonna, Justin Bieber, Shakira, BTS, Burna Boy da ƙungiyar Coldplay za su yi wasan kwaikwayo a filin wasa na MetLife Stadium da ke New Jersey.
Bugu da ƙari, za a gudanar da bikin buɗe wasan da zai ƙunshi fitattun taurari kamar Robbie Williams, Tom Cruise da Nicole Scherzinger kafin fara wasan.
Sai dai wasu na ganin tsawaita hutun rabin lokaci na iya sa ‘yan wasa su rasa kuzari, yayin da wasu kuma ke zargin cewa hakan na iya zama wata dama ta ƙara tallace-tallace a lokacin gasar.
