Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi maraba da matakin Gwamnatin Tarayya na dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2027.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana matakin a matsayin “nasara ga ‘yan Najeriya”, yana mai cewa dakatar da ƙarin kuɗin ya nuna an saurari koken jama’a.
Ya ce duk da yabawa gwamnati kan janye shirin, bai kamata a gabatar da irin wannan ƙarin kuɗi ba tun da farko, musamman a wannan lokaci da iyalai da dama ke fama da matsin tattalin arziki.
A cewarsa, ƙarin kuɗin zai ƙara wa iyaye nauyi tare da hana wasu ɗalibai samun damar ci gaba da karatunsu.
Obi ya jaddada cewa ilimi haƙƙi ne na kowane ɗan ƙasa, ba wata hanya ba ce ta gwamnati na tara kuɗaɗen shiga.
Ya kuma yi gargadin cewa ɗora ƙarin kuɗi kan ilimin matakin farko na iya ƙara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai kira ga gwamnati da ta ci gaba da zuba jari a fannin ilimi maimakon ƙara wa iyaye nauyi.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ƙara da cewa shugabanci nagari yana nuna kansa ne idan gwamnati ta saurari ra’ayin jama’a kuma ta janye manufofin da ke jefa al’umma cikin ƙunci.
A ƙarshe, Obi ya gode wa iyaye, ƙungiyoyin farar hula da sauran ‘yan Najeriya da suka nuna adawa da shirin, yana mai cewa haɗin kan jama’a ne ya taimaka wajen dakatar da ƙarin kuɗin.
