Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya kaddamar da aikin gina hanyoyin magance ambaliya da zaizayar kasa a yankin Rigasa, tare da raba takardun diyyar kusan Naira biliyan 2 ga mutane 1,000 da gidajensu za su shiga cikin aikin.
Aikin, wanda ya tashi daga Rigasa zuwa Tudun Wada a kananan hukumomin Igabi da Kaduna ta Kudu, an tsara shi ne domin kawo karshen matsalar ambaliya da ta addabi yankin tsawon kusan shekaru 40, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa kudin aikin ya haura Naira biliyan 34, yana mai cewa shi ne irinsa na farko a daukacin Arewacin Najeriya.
Ya ce gwamnatinsa ta yi alkawarin ba za ta rushe kadarorin jama’a ba sai bayan an biya su cikakkiyar diyya. Saboda haka ne aka biya kusan Naira biliyan 2 ga mutane kusan 1,000 da aikin zai shafa.
Gwamnan ya kara da cewa ya zuwa yanzu gwamnatinsa ta biya sama da Naira biliyan 5 a matsayin diyya ga mutanen da ayyukan raya kasa suka shafa, yana mai jaddada cewa ci gaba bai kamata ya lalata rayuwar jama’a ba.
A cewarsa, ci gaba ba wai gina ababen more rayuwa kadai ba ne, har ila yau yana nufin kare al’umma, dawo da martabar jama’a da kuma tabbatar da makomarsu.
Ya bayyana cewa tsawon shekaru, mazauna Rigasa da Tudun Wada sun sha fama da ambaliya da zaizayar kasa, inda gidaje, gonaki da muhimman kayayyakin more rayuwa suka lalace, tare da jefa rayuwar mutane cikin mawuyacin hali.
Gwamnan ya ce idan aka kammala aikin, zai rage hadarin ambaliya da zaizayar kasa, ya kare gidaje da kadarorin gwamnati da na jama’a, ya farfado da muhalli tare da inganta tsaron al’ummomin yankin.
Tun da farko, Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa na Jihar Kaduna, Alhaji Abubakar Buba, ya yabawa gwamnan bisa saka hannun jari a ayyukan kare muhalli a sassa daban-daban na jihar.
Ya bayyana cewa aikin Rigasa zuwa Tudun Wada zai kai tsawon kilomita 17.8, kuma idan aka kammala shi zai inganta muhalli da walwalar tattalin arzikin mazauna yankin, tare da kara matsayin Kaduna a matsayin daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen ayyukan dorewar muhalli a Najeriya.
