Jihohin Arewa 19 tare da Babban Birnin Tarayya (FCT) sun hallara a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, domin tsara sabbin hanyoyin aiwatar da shirye-shiryen kare muhalli da inganta amfani da albarkatun kasa a yankin Arewa.
An shirya taron na kwanaki uku mai taken “Tattaunawar Masu Ruwa da Tsaki da Kara Ilimi,” ne ta hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Adamawa, Bankin Duniya da shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL).
Da yake magana a gefen taron, Kodinetan ACReSAL na Jihar Adamawa, Dakta Ibrahim Chinda, ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne domin magance matsalolin muhalli da kuma inganta kula da filaye cikin dorewa.
Ya ce tsarin biyan masu kula da muhalli ta hanyar dasa bishiyoyi an fara gwada shi ne a yankin Amazon shekaru kusan 20 da suka gabata bayan an lura da yadda sare dazuzzuka ke karuwa sakamakon ayyukan noma.
A cewarsa, shirin na bai wa manoma tallafi da tsirrai domin su dasa bishiyoyi tare da kula da su, wanda hakan ke taimakawa wajen rage sare dazuzzuka, dakile zaizayar kasa da kuma dawo da yalwar kasa.
“Adamawa ita ce kadai jiha a Najeriya da ke da wuraren gwajin wannan shiri guda biyu, daya a karamar hukumar Girei, daya kuma a Numan,” in ji Chinda.
Ya kara da cewa wasu bankunan kasuwanci sun nuna sha’awar tallafawa shirin, lamarin da zai taimaka wajen fadada ayyukansa da kara yawan masu shiga cikinsa.
Chinda ya jaddada muhimmancin bishiyoyi wajen bunkasa noma mai dorewa, yana mai cewa suna kara sinadaran gina jiki a kasa, rage kwararar ruwa, samar da inuwa, kare halittu da kuma taimakawa wajen rage dumamar yanayi.
Shi ma Mataimakin Manajan Ayyuka na Africa Nature Investors Foundation, David Peter, ya ce taron zai taimaka wajen samar da sabbin hanyoyin magance matsalolin muhalli a Najeriya.
Ya bayyana cewa kula da wuraren ajiyar namun daji yadda ya kamata na iya taimakawa wajen inganta tsaro, yana mai nuni da nasarorin da ake samu a Gashaka-Gumti National Park da ke tsakanin jihohin Taraba da Adamawa har zuwa iyakar Kamaru.
A cewarsa, idan sauran wuraren ajiyar namun daji a Najeriya suka samu irin wannan kulawa, masu aikata laifuka za su rasa wuraren buya da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
