sabon Babban Limamin Masarautar Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, sabuwar mota kirar Jeep da kuma bas domin taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa na addini.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara ta ban girma da ya kai wa malamin a Ilorin ranar Talata, inda ya kuma nemi addu’o’i domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Jihar Kwara.
A cewar gwamnatin jihar, AbdulRazaq ya samu rakiyar Kwamishinan Ilimi da Raya Albarkatun Dan Adam, Lawal Olohungbe, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki na siyasa domin taya sabon limamin murnar nada shi.
Gwamnan ya bayyana cewa nada Sheikh Dasuki Imam Fulani a matsayin Babban Limamin Ilorin wata muhimmiyar nasara ce ga masarautar, domin tana nuna ci gaba, hadin kai da kuma bai wa matasa dama a cikin al’ummar Musulmi.
“Gwamnati tana tare da kai gaba daya a wannan nauyi da aka dora maka. Za mu samar maka da sabuwar mota kirar Jeep da kuma bas domin saukaka zirga-zirgarka da gudanar da ayyukanka,” in ji gwamnan.
Ya kara da cewa fitowar matashin malamin mai ilimin Azhar a matsayin sabon Babban Limami alama ce ta kokarin tabbatar da hadin kai, ci gaba da kuma hada kan al’umma ba tare da nuna bambanci ba.
AbdulRazaq ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba sabon limamin kariya, lafiya da tsawon rai tare da taimaka masa wajen gudanar da wannan babban nauyi da aka dora masa.
Ya bukaci al’ummar Masarautar Ilorin da daukacin mazauna jihar su ba sabon limamin goyon baya domin samun nasara a ayyukansa na addini.
An sanar da nadin Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani mai shekaru 42 a matsayin Babban Limami na 13 na Masarautar Ilorin a ranar 10 ga Yuni, 2026.
Haka kuma wasu fitattun malamai ciki har da Sheikh Abdulkadir Oba Sholagberu da Sheikh Sohibul Bayan sun yabawa gwamnan bisa ci gaba da tallafawa harkokin addini da shugabannin addini a jihar.
